27 Disamba 2015 - 07:56
Boko Haram: Amnesty ta Bukaci Kamaru ta yi Bayani

Kungiyar kare hakkin Bil'adama ta Amnesty International ta bukaci mahkunta a kasar Kamaru su yi bayani a kan makomar wasu mutum 130 da aka tsare sakamakon rikicin boko-haram, shekara guda da ta wuce.

Cikin wata sanarwar da ta fitar, kungiyar ta ce an tsare wasu mutane da suka hada da manya da yara 200 a kauyukan Magdeme da Double da ke arewacin kasar.

Amma daga bisani gwamnatin kasar ta ce ta tsare wasu mutum 70 da take zargin cewa 'yan boko-haram ne, amma ba ta sake cewa komai a kan sauran mutanen da take tsare da su ba.

A baya dai gwamnatin Kamarun ta musanta zargin da ake mata na azabtarwa da kashe mutanen da take zargin cewa 'yan boko-haram ne ba tare da an musu shara'a ba.288